:
Breaking News

Hisbah Ta Gayyaci Matashiyar TikTok Shatu da IB Yobe Kan Kalaman Sukar Ayyukanta

top-news
https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Jami’in kula da harkokin shoshiyal midiya na Rundunar Hisbah ta Jihar Yobe, Yusuf Muhammad Abba, ya yi karin haske kan dalilin da yasa suka gayyaci wata matashiyar TikTok mai suna Shatu, sannan daga bisani wani matashi mai suna IB Yobe.


Ga wadanda basu sani ba, A ranar Talatan 11 ga Augustar 2026, Hisbah ta kama Shatu kan wani wani bidiyo data wallafa a shafinta na TikTok, inda ta bayyana neman afuwa kan kalaman da ta yi game da Rundunar Hisbah. Bidiyon ya nuna ta tana neman afuwar rundunar tare da bayyana cewa ba za ta sake maimaita irin wadannan kalamai ba.

Bayan wannan lamari, wani matashin TikTok mai suna IB Yobe ya nuna rashin amincewarsa da yadda aka yi wa Shatu, inda ya soki matakin da Hisbah ta dauka tare da bayyana cewa, a ra’ayinsa, rundunar ba ta kyauta ba.

Hakan ya sa Hisbah ta gayyaci IB Yobe a ranar 15 ga Augustan 2026 domin jin ta bakinsa kan kalaman da ya yi. Shi ma, kamar yadda Shatu ta yi, IB Yobe ya nemi afuwar rundunar tare da alkawarin cewa ba zai sake maimaita irin wadannan kalamai ba.

Da yake magana kan lamarin, Abu Asma’u ya nuna takaicinsa kan yadda wasu mutane ke sukar ayyukan Hisbah maimakon karfafa mata gwiwa wajen gudanar da abin da ya kira aiki na addini da hidima ga al’umma.

Ya ce, “Aikin Hisbah aiki ne na hani da munmuna da umarni da kyakkyawa, wannan kuwa aiki ne dake kan kowana musulmi. Duk wanda yake ganin sasu da mukayi sukayi video ba daidai ne kuma mun musu hakanne domi. Suma video sukayi lokacin yin laifin..” Ya kuma bayyana cewa irin wannan suka ba za ta sa rundunar ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta.

Abu Asma’u ya kara da cewa, insha Allah, Rundunar Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba, za ta ci gaba da kokarin gudanar da ayyukanta bisa abin da ta yi imani da shi.

NE News – Hausa

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *