:
Breaking News

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin ƙarshe na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da mataimakansu da za su fafata a zaɓen 2027.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin ƙarshe na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da mataimakansu da za su fafata a zaɓen 2027.


Za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Jerin da INEC ta fitar ya ƙunshi ‘yan takarar Shugaban Ƙasa 18, tare da mataimakansu, daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ce ta sanya hannu kan jerin.

Daga cikin fitattun ‘yan takarar da ke cikin jerin akwai:

Bola Ahmed Tinubu APC

Atiku Abubakar ADC

Peter Obi NDC

Oluseyi Makinde APM

Sandy Ojang Onor PDP

Donald Duke PRP

Omoyele Sowore AAC

Sunday Okereke LP

Adewole Adebayo SDP

Peter Agada YPP

Nwanyanwu Daberechukwu ZLP


Sauran ‘yan takarar sun haɗa da Rufai Adekunle Omo-Aje (AA), Abbas-Bin Aliyu (ADP), Yusuf Kabiru (APP), Sunday Adenuga (BP), Adebisi Olusoji (DLA) da kuma Ada Elizabeth Frederick Okwori (NDP) da Nkem Esther Okereke (NRM).

Jerin ya nuna cewa akwai mata biyu da ke neman kujerar Shugaban Ƙasa, yayin da mata huɗu ke takarar kujerar mataimakin Shugaban Ƙasa. Su ne Peace Egobia (APP), Nafisat Usaku (DLA), Hajja Konto (LP) da Patience Key (YPP).

Dangane da shekarun ‘yan takarar, shekarun ‘yan takarar Shugaban Ƙasa sun kasance tsakanin 35 zuwa 79, yayin da na mataimakan Shugaban Ƙasa suka kasance tsakanin 35 zuwa 80.

Mafi ƙanƙantar ɗan takarar Shugaban Ƙasa shi ne Moses Adebisi na DLA, mai shekaru 35, yayin da wanda ya fi kowa shekaru yana da 79.

Haka kuma, jerin INEC ɗin ya nuna cewa babu wani ɗan takarar Shugaban Ƙasa ko mataimakinsa da ya bayyana cewa yana da nakasa.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *