RUNDUNAR SOJIN NIGERIA ZATA DAUKI SABBIN JAMI’AI MASU MATAKIN DEGREE (SSCC COURSE 50/2027)
- Repoter 11
- 16 Aug, 2026
Rundunar Sojin Najeriya ta gayyaci ’yan Najeriya da suka cancanta da su nemi gurbin shiga aikin soja a matsayin Short Service Combatant Commission (SSCC) Officers, Course 50/2027.
Rundunar ta bayyana cewa wannan dama a bude yake ga fararen hula da kuma jami’an soja masu aiki waɗanda suka cika dukkan sharuddan da aka gindaya.
Bayan kammala horo cikin nasara da kuma samun kwamishin, jami’an da aka ɗauka za su yi aiki a sassan Combat Arms, musamman Infantry da Armour Corps, da kuma Combat Support Arms, wadanda suka hada da Artillery, Engineers, Signals da Intelligence Corps.
Yadda zaka cika
Masu sha’awar neman gurbin an umurce su da su shiga tashar yanar gizo ta hukumar daukar ma’aikatan Nigerian Army, wato:
nashortservice.army.mil.ng
Daga nan sai su zabi zabin SSCC sannan su bi umarnin da aka bayar a shafin wajen kammala cikawa.
Rundunar ta yi gargadi kan shafukan bogi
Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi jama’a da su yi watsi da duk wani shafin yanar gizo ko sanarwar daukar ma’aikata da ake cewa an bude kafin wannan sanarwar ta hukuma.
Ta kuma shawarci masu neman aikin da su dogara ne kawai da bayanan da ake fitarwa ta hanyoyin sadarwa na hukumar Nigerian Army, domin kauce wa damfarar yanar gizo.
Rundunar ta kara da cewa jama’a da masu neman aikin su kasance cikin shiri domin sauraron saka makon daukar ma’aikata na hukumar bayan cikawa (recruitment jingles) da za a watsa a gidajen talabijin da rediyo bayan wannan sanarwa.
Ranar rufe cikawa
An sanya ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026 a matsayin ranar karshe ta cikawa.
Domin marin bayani, ana iya kiran lambobin waya:
07016874003
07047340295
Ana samun wadannan layuka kowace rana daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Shiga aikin soja don yiwa kasa hidima, NA
Leave a Reply
Your email address will not be published. Required fields are marked *







